Da duminsa: PDP na lallasa APC a mazabar mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Da duminsa: PDP na lallasa APC a mazabar mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Rahotannin da muke samu na nuni da cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta samu gagarumar nasara a dukkanin matakan kujerun takara a rumfar zaben mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo. PDP ta samu wannan nasarar ne a rumfar zabe mai lamba 033.

A matakin shugaban kasa, PDP ta samu kuri'u 425, yayin da APC ta samu 229.

A kujerar sanata kuwa, PDP ta samu kuri'u 414 yayin da APC ta samu 261.

Haka take a kujerar majalisar wakilan tarayya, inda PDP ta samu kuri'u 268 yayin da APC ta samu kuri'u 190.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Da duminsa: PDP na lallasa APC a mazabar mataimakin shugaban kasa, Osinbajo
Da duminsa: PDP na lallasa APC a mazabar mataimakin shugaban kasa, Osinbajo
Asali: Original

Shahararren mawakin nan da ya koma siyasa, Olubankole Wellington, (da aka fi sani da Banky W) ya samu ruwan kuri'u a mazabar, inda ya samu kuri'u 212 a matakin majalisar wakilan tarayya.

An fara kad'a kuri'a a rumfar zaben da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Asabar inda mutum na karshe ya kad'a kuri'arsa da misalin karfe 7 na yamma, yayinda aka kammala kidayar kuri'un da misalin karfe 12:20 na safiyar ranar Lahadi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel