Jam’iyyar PDP ta zargi APC da sayen kuri’u a Jihar Zamfara

Jam’iyyar PDP ta zargi APC da sayen kuri’u a Jihar Zamfara

Mun ji labari cewa ‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben jihar Zamfara watau Dr. Bello Muhammad, ya koka da cewa hukumar INEC ba ta kawo isassun kayan aikin zaben zuwa wasu bangarori na jihar ba.

Jam’iyyar PDP ta zargi APC da sayen kuri’u a Jihar Zamfara
'Dan takarar Jam’iyyar PDP yace APC na rabawa jama'a kudi wajen zabe
Asali: UGC

Bello Muhammad yayi korafi cewa kayan zabe ba su iso Kauran Namoda yadda ya kamata ba. ‘Dan takarar jam’iyyar adawar yace a wani yankin cikin Garin na Kauran Namado, takardun zabe 100 kurum aka kawo a maimakon 1000.

Haka zalika kuma, Dr. Muhammad ya bayyana cewa hukumar zabe ta gaza yin komai bayan Wakilan PDP sun kai mata korafin cewa an samu wurare fiye da 7 da babu isassun kaya. Muhammad yace da alama an shirya magudi.

KU KARANTA: An bindige Shugaban Jam’iyyar APC na Garin Dogon Daji a Sokoto

‘Dan takaran ya bayyana wannan ne bayan ya kada kuri’a sa jiya a mazabar sa da ke cikin wata Unguwa a Kudancin Maradun. Mai neman gwamnan jihar yayi ikirarin cewa ana satar kuri’a a inda jam’iyyar adawa ta ke da karfi a Zamfara.

Babban ‘dan takarar hamayyar kasar ya bayyana cewa wani Kansilan APC yana yawo yana rudar Talakawa da kudi domin su dangwalawa jam’iyyar da ke mulki a yankin. Muhammad yace ya ga wannan kuru-kuru da idanun sa.

Jam’iyyar ta PDP dai tana zargin hukumar INEC da hada kai da jam’iyyar APC mai mulki domin tafka magudi a zaben. Sai daga baya ne dai INEC ta ba jam’iyyar APC dama ta shiga zaben na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel