Wasu sun bindige Shugaban Jam’iyyar APC na Garin Dogon Daji

Wasu sun bindige Shugaban Jam’iyyar APC na Garin Dogon Daji

Labari ya iso gare mu cewa an hallaka wani daga cikin manyan jam’iyyar APC mai mulki a Garin Dogon Daji da ke cikin karamar hukumar Tsafe a cikin jihar Zamfara a Ranar Juma’ar nan da ta wuce.

Wasu sun bindige Shugaban Jam’iyyar APC na Garin Dogon Daji
An harbe wani Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara
Asali: Facebook

Kamar yadda mu ke samun labari daga jaridun kasar nan, wasu ‘yan bindiga da ba a san su bane su ka shigo Garin Dogon Daji da ke cikin shiyar Tsafe inda su ka rika harbi ko ta ina da kimanin karfe 8:00 na dare shekaran jiya.

Wadannan Miyagun mutane sun aika Alhaji Yusuf A. D wanda shi ne shugaban jam’iyyar mai mulki zuwa lahira. Jami’an ‘yan sanda na jihar Zamfara sun tabbatar da aukuwan wannan mummunan abu ta wayar tarho jiya.

KU KARANTA: Sanatan PRP Shehu Sani ya rasa akwatin zaben sa a Kaduna

Kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara, Celestine Okoye ya kai ziyara zuwa cikin gundumar Dogon Daji domin ganewa idanun sa wannan abu. Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fada mana wannan.

Bayan hallaka jagoran jam’iyya mai mulki, wadannan ‘yan bindiga sun kuma sace mutane fiye da 20 a cikin garin na Dogon Daji. Wadanda su kayi wannan aiki, sun tsere bayan sun yi awon-gaba da Bayin Allah kamar yadda mu ka ji.

Kamsilan yankin watau Alhaji Aliyu Abubakar yayi tir da wannan mummunan abu da ya faru inda ya koka da cewa matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, ta kai inda ta kai a daukacin jihar Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel