Zabe 2019: An kashe soja daya da wasu mutane 6 a jihar Rivers

Zabe 2019: An kashe soja daya da wasu mutane 6 a jihar Rivers

A yammacin yau Asabar 23 ga watan Fabrairu ne Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da rasuwar wani soja mai mukamin laftanant da aka kashe a rikicin jihar Rivers.

A baya, Premium Times ta ruwaito cewa a kalla mutane hudu ne suka rasa rayyukansu a rikicin da ya barke a jihar ta Rivers.

Sanarwar mutuwar sojan ya fito ne daga bakin sabon kakakin rundunar sojojin Najeriya, Sagir Musa.

Zabe 2019: An kashe soja daya da wasu mutane 6 a jihar Rivers
Zabe 2019: An kashe soja daya da wasu mutane 6 a jihar Rivers
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya kayar da Atiku a mazabar Obasanjo

Mr Musa ya ce mutane bakwai ne suka mutu cikinsu har da laftanant na soja yayin da wasu mutane suka kai musu farmaki lokacin da suke sintiri.

Ga wani sashi cikin sakon da Musa ya bayar a kasa:

"Sakon da muka samu daga hedkwatan soji ya bayyana cewa an kaiwa dakarun soji na 6 Division hari yayin da suke aikin sintiri domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma a karamar hukumar Akuku Toro da ke jihar Rivers.

"An kai harin ne a tsakanin gidajen Charles da Bob-Manuel da ke garin Abonnema misalin karfe 1 na ranar 23 ga watan Fabrairu.

"Maharan sunyi kwantar baune ne a wani babban titi inda suka bude wa sojojin wuta a a yayin da suke kokarin wucewa inda sojojin suka kashe 6 daga cikin maharan amma laftanant guda daya ya mutu sakamakon musayar wutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel