Yanzu-yanzu: Adams Oshiomole, Akpabio sun kawo akwatunansu

Yanzu-yanzu: Adams Oshiomole, Akpabio sun kawo akwatunansu

Shugaba jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Aliu Oshiomole, ya baiwa jam'iyyarsa nasara a zaben shugaban kasa, majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya a zaben da aka gudanar ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Jam'iyyar adawa ta PDP bata samu ko kuri'a daya ba a mazabar Adams Oshiomole a jihar Edo. Kalli sakamakon:

Oshiomole PU 01, Ward 10, Iramoh

APC: 775

PDP: 0

Hakazalika, shugaban kamfen Buhari a yankin kudu, Sanata Godswill Akpabio, ya kawo akwatinsa inda jam'iyyarsa ta APC ta samu gagarumin Nasara. Da kyar babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta samu yan kuri'u a mazabar Akpabio.

Akpabio: Ukana West, Ward 2, Unit 9

APC 1553

PDP 11

KU KARANTA: Yadda zabe ke gudana a fadin Najeriya

A bangare guda, Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam ya gaza zuwa ya kada kuri'arsa a mazabarsa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a yau Asabar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Wannan ya faru ne saboda hare-haren bama-bamai da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a wurare biyu da sanyin safiyar yau a jihar ta Yobe kamar yadda ofishin jami'in hulda da jama'a da manema labarai na Gaidam ya sanar.

Sanarwar ta ofishin ya fitar ya ce Gwamnan bai samu damar zuwa mazabarsa na garin Bukarti ba domin zabe saboda kusancin ta da garin Gaidam inda bama-baman suka tashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel