Sanata Shehu Sani ya sha kashi a akwatin Unguwar sa a hannun APC

Sanata Shehu Sani ya sha kashi a akwatin Unguwar sa a hannun APC

Mun samu labari dazu cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya sha kasa a akwatin da yayi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya da aka yi yau a Unguwar Sarki a cikin jihar Kaduna.

Sanata Shehu Sani ya sha kashi a akwatin Unguwar sa a hannun APC
Shehu Sani ya rasa akwatin yankin sa a zaben Sanata
Asali: UGC

Sanata Shehu Sani wanda yake wakiltar Mazabar tsakiyar Kaduna ya sha kashi a hannun ‘Dan takarar jam’iyyar APC watau Uba Sani a kujerar Sanata da yake kai. Shehu Sani ya samu kuri’a 51, APC kuma ta samu 236.

Har yanzu LEGIT Hausa ba ta samu labarin kuri’ar da ‘Dan takarar PDP na Sanatan yankin watau Lawal Abubakar ya samu a akwati mai lamba na 20 na Unguwar Sarki da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

KU KARANTA: 'Dan takarar Gwamnan Kano a Jam'iyyar adawa ya zabi Buhari

A kujerar ‘dan majalisa kuma, APC ta samu 240, PDP kuma ta samu 47 yayin da jam’iyyar PRP ta Sanata Shehu Sani ta samu kuri’a 28. A zaben Shugaban kasa kuma APC ta samu 292 inda jam’iyyar adawa ta samu 23.

A akwatin da gwamna El-Rufai kuma yayi zabe, PDP ta samu kuri’a 44, ita kuma APC ta samu 369 a zaben shugaban kasa. A zaben ‘dan majalisa kuma APC ta samu kuri’a 323, PDP ta samu 77, ita kuma PRP ta samu 19.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel