Zaben 2019: Boko Haram ta hana Gwamna Gaidam kada kuri'arsa

Zaben 2019: Boko Haram ta hana Gwamna Gaidam kada kuri'arsa

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam ya gaza zuwa ya kada kuri'arsa a mazabarsa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a yau Asabar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Wannan ya faru ne saboda hare-haren bama-bamai da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a wurare biyu da sanyin safiyar yau a jihar ta Yobe kamar yadda ofishin jami'in hulda da jama'a da manema labarai na Gaidam ya sanar.

Sanarwar ta ofishin ya fitar ya ce Gwamnan bai samu damar zuwa mazabarsa na garin Bukarti ba domin zabe saboda kusancin ta da garin Gaidam inda bama-baman suka tashi.

Boko Haram ta hana Gwamna Gaidam kada kuri'arsa

Boko Haram ta hana Gwamna Gaidam kada kuri'arsa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya ke gudana a Sokoto, Jigawa da Kebbi

Rahotanni da suka fito daga kafafen yada labarai sun bayyana cewa hankula sun kwanta a yanzu kuma tuni an fara fitar da sakamakon zabe a wasu sassan jihohin da aka kammala zabe da wuri.

Sakamakon zabukkan sun fara shigo daga jihohi daban-daban na Najeriya kuma ana sa ran za a kammala kidaiyar a daren yau ko kuma a gobe Lahadi kafin a sanar da sakamakon zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel