Zabe: An gano shugaba Buhari yana leken takardar zaben uwargidarsa, Aisha

Zabe: An gano shugaba Buhari yana leken takardar zaben uwargidarsa, Aisha

- Mutane sun kaure da dariya a lokacinda shugaba Buhari ke leken takardan zaben Aisha

- Shugaban kasar tare da uwargidansa sun isa wajen kada kuri’a karfe 8:00 na safe inda suka kada kuri’a a cikin yan mintoci

- Yayinda take kokarin matsawa wajen akwatin zabe bayan ta kada kuri’arta, sai shugaban kasar ya mike wuyarsa don sanin wanda uwar gidansa ta zaba

Jama’a sun kaure da dariya a safiyar Asabar a lokacinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yunkurin leken takardan zaben uwar gidansa, Aisha a yankin Sarkin Yara Ward A, a mazabar Kofa Baru polling Unit (003), a yankin karamar hukumar Gidan Niyam dake jihar Katsina.

Aisha ta kasance yar asalin Adamawa, garin babban abokin adawan mijinta, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Zabe: An gano shugaba Buhari yana leken takardar zaben uwargidarsa, Aisha

Zabe: An gano shugaba Buhari yana leken takardar zaben uwargidarsa, Aisha
Source: UGC

Shugaban kasar tare da uwargidansa sun isa wajen kada kuri’a karfe 8:00 na safe inda suka kada kuri’a a cikin yan mintoci. Sun bar wajen zaben karfe 8:11 zuwa gidansu dake GRA.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben Shugaban kasa da na yan majalisa ke gudana a jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

Majiyanmu ya rahoto cewa yayinda take kokarin matsawa wajen akwatin zabe bayan ta kada kuri’arta, sai shugaban kasar ya mike wuyarsa don sanin wanda uwar gidansa ta zaba, wanda hakan yasa mutane sun kaure da dadariya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel