Da duminsa: PDP ta samu nasara a rumfar zaben Sanwo-Olu

Da duminsa: PDP ta samu nasara a rumfar zaben Sanwo-Olu

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa jam'iyyar PDP ta samun nasara akan jam'iyyar APC a rumfar zabe ta Femi Okunnu, Lateef Jakande, Ikoyi inda dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu ya kad'a kuri'arsa a zaben shugaban kasar.

Dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, Atiku Abubakar, ya samu kuri'u 52, inda ya lallasa shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 48.

Atiku Abubakar ya samu nasara kan Muhammadu Buhari da tazarar kuri'u hudu.

Cikakken labarin na zuwa...

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Da duminsa: PDP ta samu nasara a rumfar zaben Sanwo-Olu

Da duminsa: PDP ta samu nasara a rumfar zaben Sanwo-Olu
Source: Facebook

A wani labarin; Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samun yanzu na nuni da cewa rikicin siyasa ya barke a jihar Rivers, wanda har ya zama silar mutuwar mutane akalla 15 a jihar.

Rahotannin sun bayyana cewa mutanen sun mutu ne a karamar hukumar Akuku Toru da ke jihar. Legit.ng Hausa ta tattara rahoto kan cewa rikicin ya kawo tsaikon zabe a wuraren da lamarin ya shafa.

Yan Nigeria a yau, sun fita kwansu da kwarkwatarsu domin kad'a kuri'arsu a zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya 469.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel