Zabe: 'Yan daban siyasa sun bankawa akwatunan zabe wuta a Legas

Mun samu rahoto cewa an kone wasu akwatunan zabe da ake dangwale a rumfar zabe mai lamba 18 da ke mahadar Ohafia/Ago Palace way a karamar hukumar Oshodi/Isolo da ke jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito wutar da shafi wasu akwatunan zabe da ke rumfar zabe mai lamba 23 a Baba-Ewe Street/Ago Place way.

Jami'an wucin gadi na INEC da masu al'umma da suka zo kada kuri'a duk sun tsere domin tsira da lafiyarsu da rayuwarsu.

Jami'an 'yan sandan SARS reshen jihar Legas sun garzaya wurin domin kama wadanda suka bankawa akwatunan zaben wuta.

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya ke gudana a Sokoto, Jigawa da Kebbi

Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoton, Jami'an wucin gadi na INEC da masu zabe ba su dawo rumfar zaben ba.

Kazalika, a rumfunan zabe masu lamba 035 da 036 da ke Adeneken Street/Alhaji Olusesi da kuma Adeneken Street/ Olusesi, Ago Palace an gano cewa wasu matasa da suka zo a kan babura da adaidaita sahu suna yunkurin tilastawa mutane zaben 'yan takarar da ba suyi niyya ba.

Jami'an SARS sun hallara a wurin inda suka tarwatsa bata garin ta hanyar harba hasashi a sama.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mr Zubairu Mu'azu ya tabbatar da afkuwar rikicin na Okoto inda ya ce ya bayar da umurnin a magance matsalar nan take.

Source: Legit

Mailfire view pixel