An bindige wani dan shekara 19 yayinda yake zabe a jihar Kogi

An bindige wani dan shekara 19 yayinda yake zabe a jihar Kogi

Labari da muka samu a yanzun nan ya bayyana cewa an bindige wata matashi dan shekara 19 a duniya yayinda yake kokari kada kuri’a a jihar Kogi.

An tattaro cewa a kwanan nan ne matashin mai suna Daniel Usman ya samu gurbin karatu a jami’ar jihar Kogi.

Lamarin dai ya afku ne a mazabar Ajetachi da ke yankin Anyigba, jihar Kogi.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben Shugaban kasa da na yan majalisa ke gudana a jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

A wani lamari makamancin haka mun ji cewa wasu yan baranda sun bindige mutane hudu, biyu manyan jigogin jam'iyyar All Progressives Congress APC a karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas, yankin Neja Delta.

Legit.ng ta samu labari Kakakin hukumar yan sanda na jihar Ribas Omoni Nnamdi, ya tabbatar da hakan ne bayan jam'iyyar APC ta kai kuka. Kakakin jam'iyyar APC na jihar yace: "Yan barandan PDP sun bindige jigogin jam'iyyar APC a Asarama, Cif Mowan Etete." B

anda shi, an kashe babban yayansa da kuma wani dan'uwansa a jihar. Na hudun kuma, wani mutumi ne mai suna Ignatius, dan jam'iyyar APC. Ya rasa rayuwarsa a Ajakaka, Andoni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel