Atiku ya sha alwashin amincewa da sakamakon zabe idan har aka kamanta gaskiya

Atiku ya sha alwashin amincewa da sakamakon zabe idan har aka kamanta gaskiya

- Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya sha alwashin karban sakamakon zabe Shugaban kasa idan har aka yi zabe da gaskiya

- Atiku yayi Magana ne bayan ya kada kuri’arsa a mazabar Ajiya da ke Jimeta, Yola

- Atiku yace a matsayinsa na dan damokradiyya, bashi da matsala wajen karban sakamakon zabe

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu ya sha alwashin karban sakamakon zabe Shugaban kasa idan har aka yi zabe da gaskiya.

Ya yi Magana ne bayan ya kada kuri’arsa a mazabar Ajiya da ke Jimeta, Yola.

Atiku ya sha alwashin amincewa da sakamakon zabe idan har aka kamanta gaskiya

Atiku ya sha alwashin amincewa da sakamakon zabe idan har aka kamanta gaskiya
Source: Facebook

Atiku yace a matsayinsa na dan damokradiyya, bashi da matsala wajen karban sakamakon zabe.

“Ni dan damokradiyya na gaskiya ba kamar wasu ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben Shugaban kasa da na yan majalisa ke gudana a jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

Atiku wanda yayi jawabi ga manema labarai bayan kada kuri’arsa ya jadadda cewa koda dai yana da tabbacin yin nasara, zai amshi kaye idan har zaben ya zamo babu murdiya a ciki.

Ya nuna jin dadi ga yadda masu zabe suka fito don sauke hakkin da ya rataya a wuyansa a lokacin zabe tare da fatan dukkanin jami’an zabe za su gudanar da ayyukansu cikin amana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel