Da duminsa: An bindige mutane 4 a jihar Ribas

Da duminsa: An bindige mutane 4 a jihar Ribas

Wasu yan baranda sun bindige mutane hudu, biyu manyan jigogin jam'iyyar All Progressives Congress APC a karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas, yankin Neja Delta. Legit.ng ta samu labari

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Ribas Omoni Nnamdi, ya tabbatar da hakan ne bayan jam'iyyar APC ta kai kuka.

Kakakin jam'iyyar APC na jihar yace: "Yan barandan PDP sun bindige jigogin jam'iyyar APC a Asarama, Cif Mowan Etete."

Banda shi, an kashe babban yayansa da kuma wani dan'uwansa a jihar.

Na hudun kuma, wani mutumi ne mai suna Ignatius, dan jam'iyyar APC. Ya rasa rayuwarsa a Ajakaka, Andoni.

KU KARANTA: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a fadin Najeriya

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Mista Nnamdi ya tabbatar dalabarin inda yace: "Hakane, muna da labari. Muna kokarin damke wadanda sukayi kisa kuuma munyi kokarin kwantar da kuran."

Gabanin zabe, Mista Nnamdi ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar yan sanda zasu tabbatar da zaman lafiya a jihar Ribas.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa an fara harbe-harbe a a PU 14, Ward 8, karamar hukumar Ubima ta jihar RIbas.

Ubima itace mahaifar ministan sufuri kuma dirakta janar da zaben shugaba Buhari, Rotimi Chibuike Amaechi.

Wata jami'ar hukumar FRSC ta kai kuka ga abokan aikin ta hanyar kiransu a wayar tarho domin su kawo dauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel