APC za ta amince da sakamakon zabe amma sai da sharudda - Tinubu

APC za ta amince da sakamakon zabe amma sai da sharudda - Tinubu

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce jam'iyyarsa za ta amince da duk wani sakamako da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar. Ya bada wannan tabbacin a lokacin da ya ke amsa tambayoyi ga manema labarai a rumfar da ya kad'a kuri'arsa.

Ya ce APC za ta amince da sakamakon zaben ne kawai idan aka gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi a ciki.

Da ya ke tsokaci kan yadda tsarin zabe ya ke, ya ce: "Zaben na gudana cikin nasara. Hakan ya faru sakamakon jajircewar 'yan Nigeria. Munbi hanyar da ta dace amma mai wahala wajen zaben shuwagabanninmu, ita ce hanyar demokaradiyya.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

APC za ta amince da sakamakon zabe amma sai da sharudda - Tinubu

APC za ta amince da sakamakon zabe amma sai da sharudda - Tinubu
Source: UGC

"Komai yana gudana a rumfunan zabe. Sun kasance cikin shiri da zakuwa su kad'a kuri'arsu tun makon da ya gabata amma aka dage zaben. Duk da rashin jin dadin hakan, mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu.

"Zan amince da sakamakon zaben, idan har ya kasance sahihi. Duk wani dan demokaradiyya da ba zai amince da sakamakon sahihin zabe ba, to bai cancanci a kira sa dan demokaradiyya ba. Muna a shirye mu amince da sakamakon zabe idan har sahihi ne, duk da na san cewa mu ne za mu samu nasara a zaben."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel