Yanzu-yanzu: Obasanjo ya kada kuri'arsa a Abeokuta, hotuna

Yanzu-yanzu: Obasanjo ya kada kuri'arsa a Abeokuta, hotuna

Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Aremu Obasanjo ya kada kuri'arsa a mazabarsa da ke ward 11 unit 22 a harabar gidan Olusomi da ke Abeokuta a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa.

An dai fara kada kuri'a a mazabar ne tun sa'o'i uku da suka gabata a yawancin mazabu da ke jihar ta Abeokuta.

A hirar da ya yi da manema labarai gabanin jefa kuri'arsa, Obasanjo ya yi kira ga al'umma su fito kwansu da kwarkwata su jefa kuri'arsu domin zaban shugabanin da za su jagorance su.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 7 da mutum zai yi ba tare da ya tara wa kansa gajiya ba

Yanzu-yanzu: Obasanjo ya kada kuri'arsa a Abeokuta, hoto

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayin da ake tantance katin zabensa a Abeokuta
Source: Twitter

Yanzu-yanzu: Obasanjo ya kada kuri'arsa a Abeokuta, hoto

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayin da ya ke jefa kuri'arsa cikin akwatin zabe
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel