An kama jiga-jigan jam’iyya da katunan zabe 43 a Benue

An kama jiga-jigan jam’iyya da katunan zabe 43 a Benue

Labari da muka samu a yanzu ya nuna cewa an kama wasu jami’an jam’iyyar siyasa a jihar Benue dauke da katunan zaben 43.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zaben Shugaban kasa da na yan majalisa ke gudana a fadin kasar a yau Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Jami’an da aka kama sune; Christopher Iordye wanda aka kama dauke da katunan zabe shida dayan jami’in kuma shine Terseer Iordye dauke da katunan zabe 37 duk a a mazabar makarantar sakanadare na Gbajimgba a jihar Benue.

An kama jiga-jigan jam’iyya da katunan zabe 43 a Benue

An kama jiga-jigan jam’iyya da katunan zabe 43 a Benue
Source: UGC

Sai dai ba a bayyana ainahin jam'iyyar da jami'an suke ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani lamari na daban, mun ji cewa wasu Jami’an tsaro a Kano sun barbadawa masu neman aikin malaman zabe borkonon tsohuwa yayin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisu.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Tsoro a Abuja yayinda aka zargi sojoji da cin zarafin masu zabe

A jiya da dare ne ‘yan sanda su ka watsawa masu neman aikin zabe hayakin da ke sa hawaye a cikin garin Kura da ke cikin jihar Kano.

Wani daga cikin ma’aikatan zaben ya shaidawa ‘yan jarida wannan labari jiya Juma’a. Gidan jaridar Labarai 24 ce ta rahoto mana cewa jami’an ‘yan sanda sun turnuke masu neman aikin zabe da hayaki bayan da jama’a su ka fara korafin cewa hukumar zabe na INEC ta jibge su ba tare da cewa komai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel