Duk da barazanar Boko Haram, ana fitowa zabe a yankunan Gashuwa, Damaturu da Potiskum

Duk da barazanar Boko Haram, ana fitowa zabe a yankunan Gashuwa, Damaturu da Potiskum

- Ana cigaba da kada kuri'a a kananan hukumomin jihar Yobe

- An fara kada kuri'ar ne da misalin karfe 8:09 na safiyar yau

- Ana kada kuri'ar cikin kwanciyar hankali ba tare da wata tarzoma ba

Duk da barazanar Boko Haram, ana fitowa zabe a yankunan Gashuwa, Damaturu da Potiskum

Duk da barazanar Boko Haram, ana fitowa zabe a yankunan Gashuwa, Damaturu da Potiskum
Source: Facebook

Ana cigaba da kada kuri'a a Damaturu, Potiskum da Gashua dukkanin su kananan hukumomi ne karkashin jihar Yobe.

Majiyar mu daga Damaturu babbar karamar hukumar jihar yace masu kada kuri'a a Meri award unit na 5 sun fito wajen tun misalin karfe 6:00am yayin da aka fara zaben da misalin karfe 8:09am.

Mai kula da wannan yankin Konto Ali ya bayyana cewa suna gudanar da zaben nasu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

GA WANNAN: Hare-haren Katsina: Mutanen yankin sun fara komawa Batsari a matsayin masu gudun hijira

A Gashua kuwa an fara kada kuri'a a ward din Sarkin Hausawa da misalin karfe 8:00am.

Yayin da Potiskum kuma aka fara gudanar da zaben da misalin karfe 8:50am.

Masu kawo mana rahoto sun bayyana cewa dukkanin wadannnan gurare ana gudanar da zaben lafiya babu kuma wani rahoto da suka samu na afkuwar wani abu.

A wasu yankunan dai, ana sake samun matsalar card reader, a jihar Borno kuma, an samu kayan fashewa da Boko Haram ke cillo wa cikin birnin, amma duk da haka muta suna ta fita

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel