Yadda Atiku da Titi suka dangwala nasu quri'un a yau da safe

Yadda Atiku da Titi suka dangwala nasu quri'un a yau da safe

- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP ya kada kuri'ar sa

- Ya samu rakiyar matar sa zuwa wajen zaben

- Ya jefa kuri'ar sa da misalin 10:08 na safiyar yau

Yadda Atiku da Titi suka dangwala nasu quri'un a yau da safe

Yadda Atiku da Titi suka dangwala nasu quri'un a yau da safe
Source: Facebook

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya jefa kuri'ar sa.

Atiku ya kada kuri'ar sa ne a wajen kada kuri'a dake Ajiya yankin Gwadabawa karamar hukumar jihar Adamawa da misalin karfe 10:08 na safiyar yau.

Dan takarar ya samu rakiyar matarsa Titi zuwa wajen zaben, sai manyan hadimansa da masu tsaron lafiyarsu.

GA WANNAN: Bayan Ghana, Italiya ma ta fara koro 'yan Najeriya saboda kananan laifuka daga zuwansu

Bayan da ya kada tasa kuri'ar, yayi kira ga jama'a dasu fito su kada kuri'arsu kada su kwanta a gida, domin su ceci kasar nan su kuma cika burinsa na zama shugaban kasa.

Ana sa rai dai za'a sami karuwar masu fita kada kuri'a, amma da kamar wuya Atikun ya kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, sai dai, akwai abin mamaki irin yadda aka yi a Amurka, yana iya faruwa

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel