Rashin kawo kayan zabe da wuri ya taba zuciyar masu zabe a mazabar Saraki

Rashin kawo kayan zabe da wuri ya taba zuciyar masu zabe a mazabar Saraki

Masu zabe a mazabar Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki sun koka kan jinkiri da aka samu wajen isowar jami’an INEC da kayan zabe a ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu yayinda zaben Shugaban kasa da na yan majalisa ke gudana a fadin kasar.

Mazabar na a kwatas din Agbaji da ke Ilirin, babbar birnin jihar Kwara.

Bisa ga tsarin gudanarwar hukumar zabe, ya kamata ace runfunar zabe su bude da karfe 8:00 na safe sannan su rufe da karfe 2:00 na rana.

Rashin kawo kayan zabe da wuri ya taba zuciyar masu zabe a mazabar Saraki

Rashin kawo kayan zabe da wuri ya taba zuciyar masu zabe a mazabar Saraki
Source: Depositphotos

Amma sai gashi da misalin karfe 8:23 na safe, ba’a gano jami’an INEC da kayan zabe ba a mazabun.

Wasu daga cikin masu zaben sun yi Allah wadai da jinkirin da hukumar zabe mai zaman kanta ta haddasa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Tsoro a Abuja yayinda aka zargi sojoji da cin zarafin masu zabe

A wani lamari makamancin haka, mun ji ce wa masu zabe a Lafia, jihar Nasarawa sun fara tururuwan fitowa domin kada kuri’unsu na zaben Shugaban kasa da yan majalisa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa mafi akasarin masu zabe sun isa mazabunsu a yankin tun da misalin karfe 7:00 na safe domin bin layi sannan su jira jami’an zabe.

A mazabar Bukan-sidi, an gano masu zabe tsaye cikin zumudi inda wasu suka taru a bangarori daban-daban tare da jami’an tsaro cike domin lura da yadda abubuwa ke gudana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel