Zaben 2019: Tsoro a Abuja yayinda aka zargi sojoji da cin zarafin masu zabe

Zaben 2019: Tsoro a Abuja yayinda aka zargi sojoji da cin zarafin masu zabe

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa masu zabe na korafi game da yadda sojoji da sauran hukumomin tsaro suke hana zirga-zirga a Karu, Jiwoyi, Nyanya da dukkanin kewayen Abuja kafin karfe 6:00 na safe.

Sun bayyana cewar hakan yasa suna fuskantar matsala wajen zuwa mazabunsu.

Masu zabe na korafi kan yadda ake cin zarafinsu da razanasu yayinda aka ango sojoji na dukan mutane a yankin mazabar 005, kusa da Masallaci a Karu, don kakkabewa kwamadansu hanya.

Zaben 2019: Tsoro a Abuja yayinda aka zargi sojoji da cin zarafin masu zabe

Zaben 2019: Tsoro a Abuja yayinda aka zargi sojoji da cin zarafin masu zabe
Source: Twitter

A wani lamari na daban, mun ji cewa wasu Jami’an tsaro a Kano sun barbadawa masu neman aikin malaman zabe borkonon tsohuwa yayin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisu.

KU KARANTA KUMA: Zaben yau: Jami'an INEC basu iso ba yayinda mutane ke tururuwan fitowa a Nasarawa

A jiya da dare ne ‘yan sanda su ka watsawa masu neman aikin zabe hayakin da ke sa hawaye a cikin garin Kura da ke cikin jihar Kano. Wani daga cikin ma’aikatan zaben ya shaidawa ‘yan jarida wannan labari jiya Juma’a.

Gidan jaridar Labarai 24 ce ta rahoto mana cewa jami’an ‘yan sanda sun turnuke masu neman aikin zabe da hayaki bayan da jama’a su ka fara korafin cewa hukumar zabe na INEC ta jibge su ba tare da cewa komai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel