Assha: Gwamnan Kogi ya samu tsaikon kad'a kuri'a saboda lalacewar 'Card reader'

Assha: Gwamnan Kogi ya samu tsaikon kad'a kuri'a saboda lalacewar 'Card reader'

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya samu tsaiko a lokacin da ya je kad'a kuri'arsa a rumfar zabe mai lamba 011 da ke gudanar Agassa Okene-eba Ahachi, sakamakon lalacewar na'urar tantance masu zabe (Card reader).

Gwamnan, wanda ya isa rumfar zaben tare da uwar gidansa tun karfe 8 na safiya, har zuwa karfe 9 da mintuna 10 bai samu damar kad'a kuri'ar ta sa ba sakamakon lalacewar na'urar tantance masu zaben.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Assha: Gwamnan Kogi ya samu tsaikon kad'a kuri'a saboda lalacewar 'Card reader'

Assha: Gwamnan Kogi ya samu tsaikon kad'a kuri'a saboda lalacewar 'Card reader'
Source: Facebook

Gwamna wanda ya bayyana rashin jin dadinsa akan faruwar hakan ya fice daga sahun masu zaben tare da komawa cikin motarsa, a yayin da jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke kokarin ganin ta shawo kan matsalar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa na'urar 'Card reader' guda daya ce kawai ke aiki a rumfar zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel