Zaben yau: Jami'an INEC basu iso ba yayinda mutane ke tururuwan fitowa a Nasarawa

Zaben yau: Jami'an INEC basu iso ba yayinda mutane ke tururuwan fitowa a Nasarawa

Masu zabe a Lafia, jihar Nasarawa sun fara tururuwan fitowa domin kada kuri’unsu na zaben Shugaban kasa da yan majalisa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa mafi akasarin masu zabe sun isa mazabunsu a yankin tun da misalin karfe 7:00 na safe domin bin layi sannan su jira jami’an zabe.

A mazabar Bukan-sidi, an gano masu zabe tsaye cikin zumudi inda wasu suka taru a bangarori daban-daban tare da jami’an tsaro cike domin lura da yadda abubuwa ke gudana.

Zaben yau: Jami'an INEC basu iso ba yayinda mutane ke tururuwan fitowa a Nasarawa

Zaben yau: Jami'an INEC basu iso ba yayinda mutane ke tururuwan fitowa a Nasarawa
Source: UGC

Hakazalika, a lokacin kawo wannan rahoton da misalin 8:18 na safe jami’an zabe basu iso mazabar makarantar Firamare na Lafiya ta gabas ba, sashin Ciroma da wasu mazabu a yankin ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zan taya kaina murna saboda nine zan yi nasara – Inji Buhari bayan ya kada kuri’a

Majiyarmu ta ruwaito cewa mafi akasarin mutane na nan suna jira ba tare da sun ga wani jami’in zabe ba domin fara kada kuri’arsu.

Babu jami’an INEC a Kofa Gayam, karamar hukumar Lafiya inda gwamnan jihar, Umaru Tanko Al-Makura da matarsa Dr Mairo Almakura za su kada kuri’unsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel