Shehu Sani ya bayyana dalilin sa na canja mazaba

Shehu Sani ya bayyana dalilin sa na canja mazaba

An sa ran ganin Sanata Shehu Sani mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a mazabarsa da ke Tudun Wada Kaduna domin kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar wakilai na tarayya amma ba a gan shi ba.

A maimakon hakan, Sanatan da ke takarar zarcewa a kan kujerarsa ya kada kuri'arsa ne a rumfar zabe mai lamba 20 da ke Unguwar Sarki a karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Ya kada kuri'arsa ne misalin karfe 10.25 na safiyar yau duk da cewa ya isa wurin zaben tun karfe 10 dai-dai.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 7 da mutum zai yi ba tare da ya tara wa kansa gajiya ba

Shehu Sani ya bayyana dalilin sa na canja mazaba

Shehu Sani ya bayyana dalilin sa na canja mazaba
Source: Twitter

Kafin ya kada kuri'arsa, Shehu Sani ya yi magana da manema labarai inda ya bayyana dalilin da yasa ya canja mazaba daga Tudun Wada zuwa Unguwar Sarki.

"Wannan mazabar ta fi kusa da gida na kuma na duba matsalar zirga-zirga a ranar zabe daga wannan wurin zuwa can hakan yasa na canja mazaba zuwa inda zan iya takawa da kafa in tafi wurin zabe. Mutum na iya zabe a ko'ina," inji shi.

Sanata Sani ya bayyana rashin jin dadinsa bisa jinkirin da aka samu kafin fara zaben.

Sanatan dai yana takara ne a karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party PRP bayan ya fice daga jam'iyyar mai mulki ta APC.

Babban abokin hammayarsa shine na hannun daman gwamnan jihar, Mal Uba Sani da ke takara a karkashin jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel