Jami’an tsaro a Jihar Kano sun barbadawa Turawan zabe hayaki

Jami’an tsaro a Jihar Kano sun barbadawa Turawan zabe hayaki

Mun samu labari cewa wasu Jami’an tsaro a Kano sun barbadawa masu neman aikin malaman zabe borkonon tsohuwa yayin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisu.

Jami’an tsaro a Jihar Kano sun barbadawa Turawan zabe hayaki

Yau za a zabi shugaba da 'yan majalisun tarayya a fadin Najeriya
Source: UGC

A jiya da dare ne ‘yan sanda su ka watsawa masu neman aikin zabe hayakin da ke sa hawaye a cikin garin Kura da ke cikin jihar Kano. Wani daga cikin ma’aikatan zaben ya shaidawa ‘yan jarida wannan labari jiya Juma’a.

Gidan jaridar Labarai 24 ce ta rahoto mana cewa jami’an ‘yan sanda sun turnuke masu neman aikin zabe da hayaki bayan da jama’a su ka fara korafin cewa hukumar zabe na INEC ta jibge su ba tare da cewa komai ba.

KU KARANTA: An ji labarin ganawar da Atiku yayi da wani babba a Amurka

INEC ta ajiye wadanda su ke naman su yi aikin wucen gadi a zaben na bana, ba tare da ce masu uffan ba, na tsawon lokaci. Wannan ya sa jama’a su ka fara hayaniya saboda tsoron a sauya sunayen su cikin masu aikin zaben.

Kamar yadda mu ka ji labari, jami’an tsaron Najeriyar sun fesa barkonon tsohuwa bayan ganin guna-gunin jama’a yana nema yayi yawa a gaban ofishin na hukumar zabe na kasa domin ayi maganin korafe-korafen da ake yi.

Mutum 3 ne dai su ka jikkata a lokacin da ‘yan sanda su ka watsawa jama’a hayakin mai sa hawaye. Tuni dai aka tsere da wadannan Bayin Allah zuwa wani asibiti da ke cikin Garin na Kura a jihar Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel