Da duminsa: Peter Obi, abokin takarar Atiku na jam'iyyar PDP ya kad'a kuri'arsa a Anambra

Da duminsa: Peter Obi, abokin takarar Atiku na jam'iyyar PDP ya kad'a kuri'arsa a Anambra

Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa d'an Peter Obi, abokin takarar Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya kad'a kuri'arsa a mazabarsa da ke jihar Anambra.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kad'a kuri'arsa tare da matarsa, Mr Obi ya ce akwai rashin sauri a cikin tsarin gudanar da zaben, yana mai cewa sai mutum ya dauki dogon lokaci tare da shan wahala kafin ya kad'a kuri'arsa.

Ya kuma ce zuwa yanzu zaben na gudana cikin lumana, amma ba zai iya bayar da tabbacin ko zaben zai kasance sahihi ba har sai bayan an kammala. Ya kuma yi zargin cewa ana cin zarafin mambobin jam'iyyarsu ta PDP a wasu sassa na kasar

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Da duminsa: Peter Obi, abokin takarar Atiku na jam'iyyar PDP ya kad'a kuri'arsa a Anambra

Da duminsa: Peter Obi, abokin takarar Atiku na jam'iyyar PDP ya kad'a kuri'arsa a Anambra
Source: Twitter

A wani labarin kuwa; Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana cewa ba zata iya buga wasu sabbin katunan zabe na din-din-din ga masu kad'a zaben da suka rasa katin zabensu a gobarar da ta barke a hukumar zaben a kwanakin baya a jihar Filato.

A zantawarsa da jaridar Punch a ranar Juma'a, kwamishinan hukumar INEC na jihar Filato, Mr Husseini Pai, wanda ya yi magana ta bakin shugaban sashen ilimantar da masu kad'a kuri'a, Mr Osaretin Imahiyereonbo, ya bayyana cewa karancin lokacin da aka samu kafin fara zaben kasar ya sa hukumar ta gaza buga wasu sabbin katunan masu kad'a kuri'ar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel