Yanzu Yanzu: Zan taya kaina murna saboda nine zan yi nasara – Inji Buhari bayan ya kada kuri’a

Yanzu Yanzu: Zan taya kaina murna saboda nine zan yi nasara – Inji Buhari bayan ya kada kuri’a

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace shine zai yi nasara don haka zai taya kansa murna

- Buhari ya fadi hakan ne bayan ya gama kada kuri'arsa a Daura

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jadadda cewa shine zai yi nasara a zaben da ake gudanarwa a yau Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Da aka tambaye shi ko zai mika mulki ga wanda yayi nasara idan ya fadi zabe, Shugaban kasar yace; “Zan taya kaina murna domin ni ne zan yi nasara”.

Yanzu Yanzu: Zan taya kaina murna saboda nine zan yi nasara – Inji Buhari bayan ya kada kuri’a

Yanzu Yanzu: Zan taya kaina murna saboda nine zan yi nasara – Inji Buhari bayan ya kada kuri’a
Source: Twitter

Da safiyar yau ne dai shugaba Buhari da Uwargidarsa, Aisha suka kada kuri’arsu a Daura, jihar Katsina yayinda zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokoki ke gudana.

Uwargidan Shugaban kasa, Aisha c eta fara kada kuri’arta kafin Shugaban kasar da misalin karfe 8.06 na safe, yayinda Shugaban kasar ya kada tasa kuri’ar da misalin karfe 8.10 na safe a Kofar Baru, sashin Sarkin Yara “A” a Daura.

A bangare guda, Legit.ng ta rahoto cewa jama’a sun fara yin azama a irin su Yankin Kano domin su kada kuri’ar su. A wasu wurare dai tun dare aka fara hawa layukan zabe kafin a karaso da aikin zaben.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gaidam na karkashin harin Boko Haram

Kamar yadda labari ya zo mana, Matan aure da jama’a sun soma ajiye layi ne tun kusan karfe 2:00 na dare a cikin karamar hukumar Gwarzo da ke cikin yankin Arewacin jihar Kano, su na jiran ma’aikatan zabe su karaso cikin safiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel