Ranar zabe: Wadanda katin zabensu ya kone a gobarar Filato ba za suyi zabe ba - INEC

Ranar zabe: Wadanda katin zabensu ya kone a gobarar Filato ba za suyi zabe ba - INEC

- INEC, ta bayyana cewa ba zata iya buga wasu sabbin katunan zabe na din-din-din ga masu kad'a zaben da suka rasa katin zabensu a gobarar da ta barke a ofishinta na Filato

- INEC ta sanar da cewa karancin lokacin da aka samu kafin fara zaben kasar ya sa hukumar ta gaza buga wasu sabbin katunan masu kad'a kuri'ar

- Sai dai PDP a jihar, ta yi zargin cewa gazawar INEC na sake buga wasu sabbin katunan zaben wani shiri na APC na karya lagon PDP a jihar

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana cewa ba zata iya buga wasu sabbin katunan zabe na din-din-din ga masu kad'a zaben da suka rasa katin zabensu a gobarar da ta barke a hukumar zaben a kwanakin baya a jihar Filato.

A zantawarsa da jaridar Punch a ranar Juma'a, kwamishinan hukumar INEC na jihar Filato, Mr Husseini Pai, wanda ya yi magana ta bakin shugaban sashen ilimantar da masu kad'a kuri'a, Mr Osaretin Imahiyereonbo, ya bayyana cewa karancin lokacin da aka samu kafin fara zaben kasar ya sa hukumar ta gaza buga wasu sabbin katunan masu kad'a kuri'ar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa a makwannin da suka gabata, gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC da ke karamar hukumar Quaapan, a jihar. Gobarar ta kona kayayyakin zabe, da suka hada da akwatunan zabe, injinan bayar da hasken lantarki, kundin masu kad'a kuri'a da kuma katunan zaben da ba a kai ga karba ba. Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa akalla katunan zabe 5,000 ne suka kone.

KARANTA WANNAN: Ranar zabe: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani akan jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Ranar zabe: Wadanda katin zabensu ya kone a gobarar Filato ba za suyi zabe ba - INEC

Ranar zabe: Wadanda katin zabensu ya kone a gobarar Filato ba za suyi zabe ba - INEC
Source: Twitter

INEC ta dora alhakin gobarar akan wani mai gadi da ya sha ya bugu a wannan rana.

Pai ya ce, "Idan an kammala zabe, muna bayar da tabbacin cewa zamu buga wasu sabbin katunan zaben ga wadanda na su ya kone. Sai dai har yanzu, wadanda ba su samu katunan zabensu ba sakamakon gobarar ba za su iya yin zabe a zabukan 2019 ba."

Sai dai da ta ke tsokaci kan wannan mataki na INEC, jam'iyyar PDP a jihar, ta yi zargin cewa gazawar INEC na sake buga wasu sabbin katunan zaben da suka kone na daga cikin wani shiri na jam'iyya mai mulki ta APC na karya lagon PDP a manyan wuraren da ta ke hasashen samun nasara.

A bangarenta, APC ta yi fatali da wannan zargi na PDP, tana mai bayyana zargin a matsayin hasashe maras madogara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel