Yanzu-yanzu: Bama-bamai 10 sun tashi, ana artabu tsakanin Soji da Boko Haram a Maiduguri

Yanzu-yanzu: Bama-bamai 10 sun tashi, ana artabu tsakanin Soji da Boko Haram a Maiduguri

Mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno sun shiga cikin dar da safen nan inda suka waye gari da tashi bama'bamai cikin mintuna goma.

Bama-bamai 7 sun tashi tsakanin karfe 5:50 da 6:00 na asuban nan

A yanzu haka ana jin harbe-harbe a cikin birnin Maidugurin.

Shahrarren dan jaridan yaki, Ahmed Salkida, ya bayyana cewa:

"Yan kunar bakin sun kai hare-hare cikin garin Maiduguri ta kauyuka da ke kewaye da birnin. Jami'an soji sun bude musu wuta inda suka hanasu shiga cikin gari.

Ina kyautata zaton cewa mutane zasu iya fita kada kuri'unsu amma ana bukatar tsaro sosai da duba duk wanda ke tafiya a cikin gari.".

Ku saurari cikakken rahoton...

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel