Zabe: Rundunar sojin sama ta tura jirgi mai saukar ungulu don sanya ido a Kwara

Zabe: Rundunar sojin sama ta tura jirgi mai saukar ungulu don sanya ido a Kwara

- Rundunar sojin sama ta tura jirgin tsaro mai saukar ungulu zuwa Kwara

- Hukumar sojin tace ta yi hakan ne domin domin sanya ido kan gudanarwar zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da zai gudana a yau Asabar

- Kwamandan hedkwatar rundunar sojin sama na 203 a Ilorin, Air Commodore Patrick Obeya, yayi bayanin cewa jirgin zai ta sintiri a sama domin samar da tsaro ga mazauna jihar

Rundunar sojin saman Najeriya ta tura jirgin tsaro mai saukar ungulu zuwa Kwara domin sanya ido kan gudanarwar zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da zai gudana a yau Asabar.

Kwamandan hedkwatar rundunar sojin sama na 203 a Ilorin, Air Commodore Patrick Obeya, ya bayyana hakana taron manema labarai a Ilorin a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu.

Zabe: Rundunar sojin sama ta tura jirgi mai saukar ungulu don sanya ido a Kwara

Zabe: Rundunar sojin sama ta tura jirgi mai saukar ungulu don sanya ido a Kwara
Source: Twitter

Yayi bayanin cewa jirgin zai ta sintiri a sama domin samar da tsaro ga mazauna jihar.

Obeya ya bukaci mazauna yankin da kada su tsorata, cewa jirgin mai saukar ungulun musamman zai tsaya a wasu wurare.

KU KARANTA KUMA: Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

“Za mu sanar da bayanai ga sauran hukumomin tsaro kan matakai.

“Don haka muna bukatar mazauna jihar da su san da shirinmu akan lamarin,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel