SSG din jihar Ogun ya yi hatsari, mutum daya ya mutu

SSG din jihar Ogun ya yi hatsari, mutum daya ya mutu

Sakataren gwamnatin jihar Ogun, Taiwo Adeoluwa ya yi hatsari a ranar Juma'a a hanyar Kobape da ke babban titin Abeokuta zuwa Shagamu inda aka rasa rai guda daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Adeoluwa yana tare ne da wasu mutane hudu a cikin motar kuma suna hanyarsu ta zuwa Legas ne yayin da hatsarin ya afku.

A halin yanzu ba a bayyana sunan mutumin da ya rasu da sai dai an ce daya daga cikin hadiman gwamnan jihar ne.

SSG din jihar Ogun ya yi hatsari, mutum daya ya mutu

SSG din jihar Ogun ya yi hatsari, mutum daya ya mutu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ni dan jam'iyyar APC ne duk da kasancewa ta kakakin Atiku - Buba Galadima

Rahoton ya ce sakataren gwamnatin ya samu rauni kuma an garzaya da shi zuwa Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Idi-Aba a garin Abeokuta domin yi masa magani.

Babban kwamandan hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC, Clement Oladele ne ya tabbatar da afkuwar hatsarin a hirar wayar tarho da ya yi da majiyar Legit.ng.

"Eh, da gaske ne. Su biyar ne su kayi hatsari a cikin motar. Bani da cikaken bayani a kan hatsarin sai dai a halin yanzu ana kyautata zaton mutum daya daga cikinsu ya rasu.

"SSG yana nan da ransa. An sallame shi daga asibiti. Har na yi magana da shi a waya," inji Oladele.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel