Rikicin APC da PDP a jihar Kano: An damke mutane 70, an saki Abdulmumini Jibrin

Rikicin APC da PDP a jihar Kano: An damke mutane 70, an saki Abdulmumini Jibrin

Hukumar yan sandan Najeriya a ranan Juma'a ta damke akalla yan bangan siyasa 70 dake da hannu cikin rikicin da ya faru tsakanin mabiyan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da dan majalisar wakilai, Abdulmumini Jibrin.

Da daren nan, Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa hukumar ta saki dan majalisa, Abdulmumini Jibrin bayan tsareshi a ofishinta ranan Alhamis bayan wannan rikici.

A bayan mun kawo muku rahoton cewa kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatar da cewa hukumar ta gayyaci Abdulmumini Jibrin

Abdullahi ya tabbatar da cewa mutane biyu sun rasa rayukansu, an kona motoci 20 kuma mutane 18 sun smau mumunan raunuka.

Yace: "An gayyaci Dan majalisa Jibrin Kofa, domin wasu bayanai. Akwai wasu zarge-zarge da ake masa kuma wajibi ne yayi bayani akai, shi yasa muka gayyacesa."

Abdullahi ya yi gargadi cewa hukumar yan sanda ba zatayi kasa guiwa wajen dakile dukkan masu tayar da tarzoma a jihar ba.

Ya tabbatar da cewa duk wanda aka kama da hannu cikin asarar rayuka da dukiya zai gurfana a gaban kotu muddin hukuma ta tabbatar da bincikenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel