Rundunan yan sanda ta kama jiga-jigan PDP Kebbi da Kwara

Rundunan yan sanda ta kama jiga-jigan PDP Kebbi da Kwara

Rundunan yan sanda ta kama wasu jiga-jigan babbar jam’iyyar adawar kasar wato Peoples Democratic Party (PDP), a jihohin Kebbi da Kwara.

Jami’an tsaron sun kama jigon na PDP a Kebbi, Cif Emeka Okafor sannan suka wuce da shi Abuja.

Har ila yau rundunan sun kama dan takaran kujerar majalisar dokoki na yankin kudancin Kwara a karkashin jam’iyyar PDP, sanata Rafiu Ibrahim bisa zargin kasancewa da hannu a rikicin siyasa.

Kakakin rundunan yan sanda reshen jihar Kebbi, DSP Nafiu Muhammed ne ya tabbatar da kamun Cif Okafor.

Rundunan yan sanda ta kama jiga-jigan PDP Kebbi da Kwara

Rundunan yan sanda ta kama jiga-jigan PDP Kebbi da Kwara
Source: Depositphotos

Yace an kama jigon na PDP ne bisa laifin siyan kuri’u sannan aka tafi da shi Abuja don ci gaba da bincike.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Saidu Haruna yayinda yake ganawa da manema labarai ya bayyana cewa an kama Cif Okafor ne saboda ya ki barin jam’iyyar PDP.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Sufeto Janar na yan sanda ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a fadin kasar

Ya kara da cewa shuwagabannin jam’iyyar sun tafi ofishin yan sanda don sauraran laifin da ya aikata da kuma masaniyan inda aka kai shi.

Shugaban jam’iyyar PDP ta bayyana cewa jam’iyyar ta bada umurni ga lawyanta da ya daukaka rubutacciyar kara akan hukumar yan sanda dangane da kamun Cif Okafor.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel