Buhari ya isa Katsina gabannin zaben Shugaban kasa

Buhari ya isa Katsina gabannin zaben Shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu ya isa Katsina a hanyarsa ta zuwa Daura, mahaifarsa, inda zai kada kuri’a zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Jirgin Shugaban kasa ne ya kwashi Shugaban kasar da matarsa, Aisha, da wasu hadimansa inda suka sauka a filin jirgin Umar Musa Yar’Adua, Katsina da misalign karfe 3.25pm, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito (NAN).

Shugaban kasar ya samu tarba daga Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, karamin ministan sufurin jiragen sama, adi Sirika, mambobin majalisar dokokin jihar Katsina, shugabannin hukumomin tarayya a jihar da sauran manyan gwamnati. Shugaban kasar ya bar filin jirgin a cikin jirgi mai saukar ungulu zuwa Daura da misalin 3.50pm.

A chan Daura ana sanya ran dan takarar Shugaban kasar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben ranar Asabar zai shiga sahun sauran masu zabe a mazabar Kofar Baru 003, Sarkin Yara, Daura jihar Katsina domin kada kuri’arsa.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Sufeto Janar na yan sanda ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a fadin kasar

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Alhamis 21 ga watan Fabrairu ne shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Yobe, Alhaji Sani Inuwa Nguru ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC.

Nguru ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa tare da jigo a jam'iyyar APC ma jihar Yobe Mohammed Yahuza.

Tsohon shugaban na PDP ya shaidawa manema labarai cewa ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne domin ya jadada mubaya'arsa a gare shi tare da bayyana masa cewa ya komo gida.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel