Zabe: Sufeto Janar na yan sanda ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a fadin kasar

Zabe: Sufeto Janar na yan sanda ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a fadin kasar

Inspecta janar na rundunar yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya ba da umurni ga jami’an rundunar da su inganta matakan tsaro a fadin kasar kafin zaben shugaban kasa da na majalisa.

Har ila yau shugaban rundunar ya umurci a tura Mataimakan Sufeto Janar (DIG) a yankunan kasar da su tabbatar da isasshen gudanarwa da sanya wa yan sanda idanu a lokacin zabe.

Adamu ya cigaba da kira ga mataimakan Sufeto janar na police da kwamishinoni da su karfafa matakan tsaro a yankunan da aka tura su domin yin aiki.

Zabe: Sufeto Janar ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a fadin kasar

Zabe: Sufeto Janar ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a fadin kasar
Source: UGC

Ya kuma gargadi jami’an yan sanda da aka tura fadin kasar da su nisanta daga harkar siyasa inda ya kara da cewa ba zai karbi duk wani rashin bin doka daga kowa ba.

Hakan na kunshe ne a wani jawabin da kakain rundunan yan sanda ACP Frank Mba yayi a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu ta kama wani mamba na majalisar wakilai mai wakiltan Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, kan harin da aka kai wa tawagar tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso.

Wasu da ake zargin yan daba ne magoya bayan dan majalisar ne suka kai hari ga ayarin Kwankwaso. Anyi zargin cewa yan iskan sun yi wata hanya zuwa kauyen Kofa kawanya sannan suka yi yunkurin hana masu wucewa bi ta kauyen.

Akalla mutane biyar aka kashe, yayinda wasu da dama suka ji rauni lokacin da bangarorin biyu suka kara.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel