Sarki Sanusi ya gargadi yan siyasa akan zaman lafiya bayan rikicin da ya barke tsakanin yan APC da PDP

Sarki Sanusi ya gargadi yan siyasa akan zaman lafiya bayan rikicin da ya barke tsakanin yan APC da PDP

Sarkin Kano, Alhaji Muhhammadu Sanusi II, ya bayyana rikice-rikice da ake yawan samu tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party a matsayin abun bakin ciki da damuwa.

Sarki Sanusi yayi magana ne a ranar Juma’a, yayinda yake jawabi ga manema labarai a fadar sa da ke Kano, bayan rikici da ya auku tsakanin magoya bayan APC da PDP yayinda suke gudanar da yakin neman zabe a karamar hukumar Bebeji a jihar.

Ya roki magoya bayan jam’iyyan da masu siyasa a jihar da su daina siyasar tashin hankali da bangan siyasa. Don tabbatar da kwanciyar hankali a wajen gudanar da zabbukan kasa.

Sarki Sanusi ya gargadi yan siyasa akan zaman lafiya bayan rikicin da ya barke tsakanin yan APC da PDP

Sarki Sanusi ya gargadi yan siyasa akan zaman lafiya bayan rikicin da ya barke tsakanin yan APC da PDP
Source: Twitter

Basaraken yayi kira ga jami’an tsaro a jihar da su tsaurara kokarinsu a wajen gano wadanda ke da hannu cikin abun al’ajabin da ya faru sannan su tabbatar an hukunta masu laifi.

KU KARANTA KUMA: Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP

Ku tuna cewa a ranar Alhamis ne rikici ya barke tskanin magoya bayan APC da PDP a kauyen Tofa, Bebeji, wanda yayi sanadiyan mutuwar mutane biyar, sannan da dama suka ji rauni.

Kakakin yan sanda reshen jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatar da konewar motoci 20 sannan an faffasa motoci 18.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel