Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama dan majalisa Jibrin kan harin da aka kai wa Kwankwaso

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama dan majalisa Jibrin kan harin da aka kai wa Kwankwaso

Rundunar yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu ta kama wani mamba na majalisar wakilai mai wakiltan Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, kan harin da aka kai wa tawagar tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso.

Wasu da ake zargin yan daba ne magoya bayan dan majalisar ne suka kai hari ga ayarin Kwankwaso. Anyi zargin cewa yan iskan sun yi wata hanya zuwa kauyen Kofa kawanya sannan suka yi yunkurin hana masu wucewa bi ta kauyen.

Akalla mutane biyar aka kashe, yayinda wasu da dama suka ji rauni lokacin da bangarorin biyu suka kara.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama dan majalisa Jibrin kan harin da aka kai wa Kwankwaso

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama dan majalisa Jibrin kan harin da aka kai wa Kwankwaso
Source: Depositphotos

An kuma kona gidan dan majalisar, yayinda aka kona motoci sama da 10 kurmus.

An tattaro cewa mataimakin sufeto janar na yan sanda dake Zone 1, Dan Bature da kwamishinan yan sandan jihar, Mohammed Wakili a ranar Juma’a sun ziyarce wajen da abun ya afku sannan suka yi umurnin kama dan majalisar.

KU KARANTA KUMA: Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa a yanzu haka dan majalisar na amsa tambayoyi daga hannun yan sanda a hedkwatar rundunar da ke Bompai.

An kuma tattaro cewa gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje a ranar Laraba ya roki kwamishinan yan sanda da kada a bari Kwankwaso ya kai gangaminsa na karshe, amma kwamishinan yace ba zai iya hana tsohon gwamnan yancinsa ba idan har babu kwakwaran dalili.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel