Kiris-kafin-zabe: Shugaba Buhari ya samu karin goyon baya daga wata kungiya

Kiris-kafin-zabe: Shugaba Buhari ya samu karin goyon baya daga wata kungiya

Wasu 'yan Najeriya 'yan kasuwa dake zaune a garin Abuja sun bayyana mubayi'ar su tare da cikakken goyon bayan su ga tazarcen shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a zaben da za'a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban kungiyar ta 'yan kasuwar a garin na Abuja, Alhaji AdamuHassan ne dai ya yi wannan kira ne jiya Alhamis a ofishinsa dake kasuwar Wuse yayin gabawarsa da manema labara in da ya ce su fa game da zaben Shugaba Buhari babu gudu babu ja baya.

Kiris-kafin-zabe: Shugaba Buhari ya samu karin goyon baya daga wata kungiya

Kiris-kafin-zabe: Shugaba Buhari ya samu karin goyon baya daga wata kungiya
Source: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama mota shakare da kayan zabe

A cewar sa, su dai dama can a shirye suke, tun da farko sun umarci mambobin su da su je su yi rijista, kuma suka je suka yi, da lokacin karba ya yi haka zalika suka umarce su da su je su karba kuma suka je suka karba yanzu kuma suka shirya don zabar shugaban kasar.

A wani labarin kuma, Wani babban shehin malamin addinin Islama a Arewacin Najeriya mai suna Sheikh Abdulhakami Muntaka Kumasie ya jawo hankalin masu zabe da cewa lallai ne su kara tunanin mutane nagari da suke da kyakkyawar tarihi a cikin al’umma, ba wadanda suka fito domin neman shuganci ko kuma wakilci kawai ba.

Malamin dake zaune a garin Zariya ya kuma shawarce su da su yi anfani da iliminsu da kuma sanin da suka yi na sanin yadda shugabanci ya ke, da su zabi ‘yan takara nagari a duk zabukan da za a yi a wannan shekara ta 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Online view pixel