Rikicin Kaduna: Uwar gidan shugaba Buhari, Aisha ta raba kayayyakin tallafi

Rikicin Kaduna: Uwar gidan shugaba Buhari, Aisha ta raba kayayyakin tallafi

- Hajia Aisha Muhammadu Buhari ta rarraba kayayyakin jin-kai na miliyoyin kudi ga wadanda rikicin karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna ya shafa

- Uwar gidan shugaban kasar wacce ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa al'ummar karamar hukumar ta yi Addu'ar Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba

- Mrs Buhari ta bayar da tabbacin cewa, za a cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su gaban shari'a

Uwar gidan shugaban kasa, Hajia Aisha Muhammadu Buhari ta rarraba kayayyakin jin-kai na miliyoyin kudi ga wadanda rikicin karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna ya shafa, rikicin da ya jawo asarar sama da rayuka 130.

Wannan tallafin na ta, ya biyo bayan matsayinta kan harin da aka kai, na cewar Abun ayi Allah-wadai ne, ganin irin adadin al'ummar Adara da Fulani da suka rasa rayukansu, tana mai addu'ar Allah ya jikansu tare da kare faruwar hakan a gaba.

KARANTA WANNAN: Bayani dalla-dalla: Ganduje ba zai iya tarawa Buhari kuri'u 5m ba - Kididdiga

Rikicin Kaduna: Uwar gidan shugaba Buhari, Aisha ta raba kayayyakin tallafi

Rikicin Kaduna: Uwar gidan shugaba Buhari, Aisha ta raba kayayyakin tallafi
Source: Depositphotos

Da take rarraba kayayyakin tallafin ga wadanda suka tsira da rayukansu a Maraban Kajuru da matsallakar layin dogo (Railway Crossing), duka a cikin karamar hukumar Kajuru, Mrs Buhari ta bayar da tabbacin cewa, za a cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su gaban shari'a.

Da ta samu wakilcin makusanciyarta, Hajiya Binta Muazu, uwar gidan shugaban kasar ta shaidawa al'ummar Fulani da na Adara da rikicin ya shafa, cewar Allah ya san dalilin da ya sa ya hada su zama a waje daya, domin haka, ya zama wajibi a garesu su rungumi zaman lafiya da kaunar juna.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel