Wanda musulmai yakamata su zaba ya shugabance su ranar Asabar - Wani malami a Zariya

Wanda musulmai yakamata su zaba ya shugabance su ranar Asabar - Wani malami a Zariya

Wani babban shehin malamin addinin Islama a Arewacin Najeriya mai suna Sheikh Abdulhakami Muntaka Kumasie ya jawo hankalin masu zabe da cewa lallai ne su kara tunanin mutane nagari da suke da kyakkyawar tarihi a cikin al’umma, ba wadanda suka fito domin neman shuganci ko kuma wakilci kawai ba.

Malamin dake zaune a garin Zariya ya kuma shawarce su da su yi anfani da iliminsu da kuma sanin da suka yi na sanin yadda shugabanci ya ke, da su zabi ‘yan takara nagari a duk zabukan da za a yi a wannan shekara ta 2019.

Wanda musulmai yakamata su zaba ya shugabance su ranar Asabar - Wani malami a Zariya

Wanda musulmai yakamata su zaba ya shugabance su ranar Asabar - Wani malami a Zariya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Jahohi 12 da za'ayi gumurzu tsakanin Buhari da Atiku

Haka zalika Shehin malamin ya kuma yi kira ga duk wani shugaba da wakilai da aka zaba ko kuma da za a zaba, da su rike amanar da aka dora ma su, domin shirin amsa tambayoyin da za a yi ma su a gobe bayan sun sauka daga matsayin da aka zabe su,

Sheikh Malam Abdulhakami Kumasie ya ci gaba da cewar, babbar matsalar da ta ke addabar siyasa a wannan lokaci da ake ciki, shi ne rashin samun shugabanni da kuma wakilai nagari da suke tunanin al’ummar da suke wakilaci da kuma shugabanci.

A nan ne Malamin addinin musuluncin ya kara da cewar, mafiya yawan wadanda ake zaba a wannan lokaci, da kuma wadanda aka zaba a ‘yan shekarun baya, babu tunanin wadanda suka zabe su, sai dai tunanin kansu a madafun ikon da suke, tun daga jiha ya zuwa tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel