Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP

Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP

- Shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus yace jam’iyyar na da tabbacin lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu

- Secondus ya gargadi jami’an tsaro da kada su razana mutane a wuraren zabe a lokacin zabe

- Ya kuma bukaci mutane da su yi watsi da duk wani barazana da za a yi masu

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus yace jam’iyyar na da tabbacin lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Secondus, wanda ya gana da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya gargadi jami’an tsaro da kada su razana mutane a wuraren zabe a lokacin zabe.

Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP

Muna da tabbacin cewa zamu lashe zaben shugaban kasa a gobe - PDP
Source: UGC

A cewar Secondus, “Ina bukatar ku yan Najeriya da kada ku sanya tsoro a zukatarku, kawai ku mayar da hankulanku akan wasa, wanda ita ce nasarar da zata zo a ranar Asabar.

"Dole Rundunar sojoji su yi biyayya ga dokokin da aka tsara musu. Kada a jasu cikin harkar siyasa. Duk wani kashe-kashe zai jawo hankalin kotun ICC.

“Najeriya ta kasance cikin wani irin hali har na tsawon shekaru hudu. Amman idan Atiku ya zama shugaban kasa, zai tabbatar Najeriya ta farfado."

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Sauya shekar da ake samu gab da zabe alamun nasara ne ga APC - Buni

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, wani tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Stanley Osifo a ranar Alhamis ya nuna goyon bayan shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda yake mika sanarwa akan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mista Osifo, wanda ya kasance dan Jihar Edo, ya bayyana wa yan jarida a taron manema labarai a Legas cewa zai bar jam’iyyar PDP tare da akalla magoya baya “miliyan 10” bayan gane cewa ba jam’iyyar bace mafi alkhairi wajen tabbatar da cigaban kasar.

Sanarwar Mista Osifo ya zo ne bayan yan takara 12 sun tsayar da shugaban kasa Buhari akan kudurinsa na sake neman takara.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel