Yanzu-yanzu: Daga karshe, INEC ta sanya APC a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: Daga karshe, INEC ta sanya APC a jihar Zamfara

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayyana cewa zata sanya sunayen yan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a takardan kuri'ar jihar Zamfara.

Hukumar ta alanta hakan ne a wani jawabi da shugaban kwamitin labarai da ilmantar da masu zabe, Mr Festus Okoye, ya saki ranar Juma'a, 22 ga watan Febrairu, 2019.

Mun kawo muku rahoton cewa wata kotun daukaka kara dake zaune a birnin tarayya Abuja ta yanke sabon hukuncin kan dambarwan fitar da yan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Zamfara.

Kotun daukaka karan ta yi watsi da shari'ar babban kotun tarayya da ke Abuja wacce ta halaltawa hukumar gudanar da zabr ta kasa mai zaman kanta INEC hana jam'iyyar APC fitar da yan takara a zaben 2019 da zai gudana a ranan 23 ga watan Febrairu da 9 ga watan Maris, 2019.

An dade ana jeka ka dawo tsakanin hukumar INEC da jam'iyyar APC kan rashin gudanar da zaben fidda gwani kafin ranan INEC ta kulle. Tun lokacin suka dinga safa da marwa a kotuna daban-daban.

Kalli jawabinsa:

Yanzu-yanzu: Daga karshe, INEC ta sanya APC a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: Daga karshe, INEC ta sanya APC a jihar Zamfara
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel