Yana faruwa yanzu: Shuwagabannin tsaro sun saka labule kan zaben gobe Asabar

Yana faruwa yanzu: Shuwagabannin tsaro sun saka labule kan zaben gobe Asabar

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa shugaban tsaro na kasa (CDS), Janar Gabriel Olonisakin, na kan ganawar gaggawa ta sirri da shuwagabannin tsaro da suka hada da sifeta janar na rundunar 'yan sanda (IGP) da sauran shuwagabannin hukumomin tsaro na kasar.

Legit.ng Hausa ta samu rahoton cewa taron na gudana ne a ofishinsa da ke shelkwatar tsaro a Abuja, wanda ya samu wakilcin hafsan rundunar sojin kasa (COAS), Laftnal Janar Tukur Buratai, hafsan rundunar sojin ruwa (CNS), Admiral Ibok-Ette Ibas da kuma hafsan rundunar sojin sama (CAS), Air Marshall Sadiq Abubakar.

Legit ta ruwaito cewa taron yana gudana ne domin kammala dukkanin wasu shirye shirye da tuni dama hukumomin tsaron suka fara, domin ganin an gudanar da zaben ba tare da tashin hankula ba.

KARANTA WANNAN: Ta faru ta kare: Kungiyoyin Yarabawa 25 sun yanke hukunci, sun goyi bayan Buhari/Osinbajo

Yana faruwa yanzu: Shuwagabannin tsaro sun saka labule kan zaben gobe Asabar

Yana faruwa yanzu: Shuwagabannin tsaro sun saka labule kan zaben gobe Asabar
Source: UGC

Haka zalika, daga cikin wadanda suka halarci taron wanda ake kan tattauna batun tsaro da kuma shirye shiryen da aka yi domin ganin an gudanar da zaben kasar lami lafiya ba tare da samun matsalar tsaro ba, sun had'a da Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu; Darakta Janar na rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi; Darakta Janar, hukumar tsaro ta kwararru (NIA), Ahmed Abubakar da kuma shugaban hukumar tsaro ta CDI, Air Vice Marshall Ahmed Usman.

Taron wanda ya fara da misalin karfe 12:30 na rana, ya samu halartar shuwagabannin sashen horaswa na rundunar sojin kasa, sojin ruwa, da sojin sama da kuma na hukumomin tsaro na 'yan sanda, DSS, DIA da NIA.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel