Ana gab da zabe: Tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya koma APC

Ana gab da zabe: Tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya koma APC

Wani tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Stanley Osifo a ranar Alhamis ya nuna goyon bayan shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda yake mika sanarwa akan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mista Osifo, wanda ya kasance dan Jihar Edo, ya bayyana wa yan jarida a taron manema labarai a Legas cewa zai bar jam’iyyar PDP tare da akalla magoya baya “miliyan 10” bayan gane cewa ba jam’iyyar bace mafi alkhairi wajen tabbatar da cigaban kasar.

Sanarwar Mista Osifo ya zo ne bayan yan takara 12 sun tsayar da shugaban kasa Buhari akan kudurinsa na sake neman takara.

A gab da zabe: Tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya koma APC

A gab da zabe: Tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya koma APC
Source: UGC

Ko da yake Mista Osifo, dan shekaru 42, ya kasance matashi daga cikin yan takaran shugaban kasanrkafin zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Oktoba a shekarar da ya gabata, an dauke shi tamkar dan leken asiri a jam’iyyar, inda yayi ikirarin cewa karya ake masa.

A daren ranar Alhamis, Mista Osifo ya jinjina wa gwamnatin wacce APC ke jagora inda ya yi la’akari da nasarorin da ta samu sannan ya bukaci yan Najeriya da su zabi jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Sauya shekar da ake samu gab da zabe alamun nasara ne ga APC - Buni

Shugaban jam’iyyar All Progressives Party (APC), Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ba ta da niyan yin magudi a zaben kasar mai zuwa. Yace jam’iyyar ba za ta lamunta da yan iska da satar akwati a lokacin zaben ba, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Ya yi jawabin ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairu a Benin yayinda yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar sirri da yayi da shugabannin jam’iyyar daga kananan hukumomi 18 na jihar Edo.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel