An kama wani mutumi dauke da daruruwan katin zabe yayin da zabe ya rage saura kwana 1

An kama wani mutumi dauke da daruruwan katin zabe yayin da zabe ya rage saura kwana 1

Jami’an hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi, NDLEA sun samu nasarar kama wani mutumi mai suna Okon Bassey dauke da daruruwan katunan zabe da suka kai guda dari biyu da arba’in da hudu, 244 a garin Akwa Ibom.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an sun gano kudi naira dubu dari uku da goma, N310,000 daga hannun wannan mutumi, wanda suka yi ram da shi a karamar hukumar Mbo ta jahar Akwa Ibom.

KU KARANTA: Jerin garuruwa guda 10 da miyagun yan bindiga suka tasa a mahaifar shugaba Buhari

Shgaban NDLEA na kasa, Malam Abdullahi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Juma’a, inda yace tuni sun mika barawon katunan zaben ga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC don cigaba da bincike.

Bugu da kari shugaban yace sun tashi wasu dandalin yan shaye shaye guda 35 a cikin garin Kano, sa’annan yace sun kama dillalan wiwi guda 120 a jahar Akwa Ibom, inda suka kwato tabar wiwi da yawanta ya kai kilo 51, hodar iblis giram 17, kwayar hero giram 259, Tramadol gm 500, daga wajensu.

“Duk da matsalar da muke fuskanta na karancin ma’aikata da kuma ababen hawa, amma jami’anmu suna iya kokarinsu wajen yaki da masu ciniki da shan kayan maye, tare da kai samame a mafakar yan daba.

“A satin data gabata an kashe mana jami’ai guda hudu, wanda muke zargin dillalan kwayoyi ne suka kashesu a garin Ifon na jahar Ondo, yayin da suke aikin binciken wasu kwayoyi da aka yi safararsu daga jahar Edo zuwa Arewacin Najeriya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel