APC ba ta da niyar yin magudin zabe – Oshiomhole

APC ba ta da niyar yin magudin zabe – Oshiomhole

- Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ba ta da niyan yin magudi a zaben kasar mai zuwa

- Oshiomhole ya ce ba za su lamunta da yan iska da satar akwati a lokacin zaben ba

- Jigon na APC yace Buhari ya tabbatar da cewar shi shugaba ne mai aminci abun yarda don haka ya cancanci kamala zango na iyu domin ci gaban ajandarsa a kasar

Shugaban jam’iyyar All Progressives Party (APC), Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ba ta da niyan yin magudi a zaben kasar mai zuwa.

Oshiomhole ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ba za ta lamunta da yan iska da satar akwati a lokacin zaben ba, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

APC ba ta da niyar yin magudin zabe – Oshiomhole

APC ba ta da niyar yin magudin zabe – Oshiomhole
Source: Facebook

Ya yi jawabin ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairu a Benin yayinda yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar sirri da yayi da shugabannin jam’iyyar daga kananan hukumomi 18 na jihar Edo.

Oshiomhole yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar shi shugaba ne mai aminci abun yarda don haka ya cancanci kamala zango na iyu domin ci gaban ajandarsa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Sai kayi bayanin lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi – Jigon PDP ga Buhari

Hakazalika da yake jawabi, Gwamna Godwin Obaseki yace gwamnatinsa ta samu tarin nasarori a cikin dan kankanin lokaci saboda goyon bayan da yake samu daga Shugaban kasar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel