Bayani dalla-dalla: Ganduje ba zai iya tarawa Buhari kuri'u 5m ba - Kididdiga

Bayani dalla-dalla: Ganduje ba zai iya tarawa Buhari kuri'u 5m ba - Kididdiga

Bisa kididdiga, alkawarin da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dauka, na samawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri'u miliyan biyar na al'ummar jihar a zaben shugaban kasar, ba zai cika ba. Alkawarin gwamnan ba zai cika ba saboda gibin akalla kuri'u 303,253.

Wata kididdiga da jaridar TheCable ta gudanar, ta hanyar amfani da alkaluman masu kad'a kuri'a da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta saki, ya nuna cewa jihar Kano na da mutane 5,457,747 da suka yi rejista, yayin da mutane 4,696,747 ne kawai suka karbi katin zabensu na din-din-din. A dauka cewa dukkanin masu kad'a kuri'ar za su zabi Buhari, duk da hakan, alkawarin Ganduje ba zai cika ba saboda samun gibin kuri'u 303,253.

A zaben shekarar 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 1.9m a jihar Kano, kuma ya kasance mai samun nasara a jihar tun daga 2003, shekarar farko da ya fara tsayawa takarar shugabancin kasar.

KARANTA WANNAN: Ta faru ta kare: Kungiyoyin Yarabawa 25 sun yanke hukunci, sun goyi bayan Buhari/Osinbajo

Bayani dalla-dalla: Ganduje ba zai iya tarawa Buhari kuri'u 5m ba - Kididdiga

Bayani dalla-dalla: Ganduje ba zai iya tarawa Buhari kuri'u 5m ba - Kididdiga
Source: UGC

A jihar Legas kuwa, an samu sabbin masu kad'a kuri'a 1.7m da suka yi rejista, jihar da aka fi samun karin masu jefa kuri'a a fadin kasar. A shekarar 2015, mutane 3,799,274 ne suka karfi katin zabensu na din-din-din, sabanin mutane 5,531,389 da suka karba a wannan shekarar ta 2019.

Wannan sabon alkaluman masu kad'a kuri'ar da INEC ta saki ya tabbatar da cewa adadin mutanen da suka karbi katin zabensu na din-din-din a fadin kasar, zuwa 11 ga watan Fabreru, ya kai 72,775,585 daga cikin mutane 84,004,084 da suka yi rejista.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel