Zaben 2019: Sauya shekar da ake samu gab da zabe alamun nasara ne ga APC - Buni

Zaben 2019: Sauya shekar da ake samu gab da zabe alamun nasara ne ga APC - Buni

Dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya bayyana sauya shekar da Shugaban PDP a jiharm Alhaji Inuwa Nguru yayi gab da zabe zuwa jam’iyyarsa a matsayin wani Karin nasara gare su.

Legit.ng ta tattaro cewa Buni ya fadi hakan ne a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Damaturu, babbar birnin jihar Yobe.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta kawo inda Bun ice cewa Nguru ya dawo APC saboda aminta da yayi don kansa cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar na aiki ne da gaske domin ci gaban kasa sannan kuma ganin cewa sune suka fi dacewaa da damokradiyyar Najeriya.

Zaben 2019: Sauya shekar da ake samu gab da zabe alamun nasara ne ga APC - Buni

Zaben 2019: Sauya shekar da ake samu gab da zabe alamun nasara ne ga APC - Buni
Source: UGC

Buni ya kara da cewa Yob eta amfana sosai daga manyan ayyuka ciki arda kamala hayar samun wutar lantarki na 330KVA, babban titin Nguru-Gashua-Bayamari, haarkar ilimi da kuma na lafiya daga matakin gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 8 da Buhari ya fadi a jawabin da yayiwa jama’a gabannin zaben Shugaban kasa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Alhamis 21 ga watan Fabrairu ne shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Yobe, Alhaji Sani Inuwa Nguru ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC.

Nguru ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa tare da jigo a jam'iyyar APC ma jihar Yobe Mohammed Yahuza.

Tsohon shugaban na PDP ya shaidawa manema labarai cewa ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne domin ya jadada mubaya'arsa a gare shi tare da bayyana masa cewa ya komo gida.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel