Tsugune-bata-kare ba: Sanata Marafa yayi sharhi kan hukunci kotu na shigar APC zabe a Zamfara

Tsugune-bata-kare ba: Sanata Marafa yayi sharhi kan hukunci kotu na shigar APC zabe a Zamfara

Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar Gwamna takwas a karkashin inuwar jam'iyyar APC a jihar Zamfara, kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, Sanata Kabir Garba Marafa ya bayyana cewa har yanzu babu ‘yan takarar APC a jihar Zamfara.

Wannan furucin dai na Sanata Marafa yayi shi ne da yake yiwa wakilin majiyar mu karin haske biyo bayan hukuncin da a ke ta yawo da shi na kotun daukaka kara wanda tawagar alqalai uku qarqashin Mai Shari’a Abdul Aboki ta yanke hukunci a jiya Alhamis.

Tsugune-bata-kare ba: Sanata Marafa yayi sharhi kan hukunci kotu na shigar APC zabe a Zamfara

Tsugune-bata-kare ba: Sanata Marafa yayi sharhi kan hukunci kotu na shigar APC zabe a Zamfara
Source: UGC

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Katsina

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kotun daukaka karar ta yi watsi da wani hukunci da babbar kotun tarayya ta yi a ranar 25 ga watan Janairun 2015 inda ta goyi bayan INEC kan rashin amsan ‘yan takara daga jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara.

Sai dai shi da yake karin haske kan batun, Sanata Kabir Marafa ya ce, “Lallai babu wani abu da ya canza. Tuni lauyoyinmu suna nazarin wannan hukunci domin yau mu turawa INEC matsayarmu.

Amma kafin nan, yana da kyau a fahimci cewa kotun daukaka karar ba wai cewa ta yi INEC ta amshi ‘yan takara daga Zamfara ba, a’a wani yanki ne na hukunci aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel