Sai kayi bayanin lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi – Jigon PDP ga Buhari

Sai kayi bayanin lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi – Jigon PDP ga Buhari

- Wani jigon jam’iyyar PDP ya bukaci Buhari da yayi karin haske akan lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi idan har aka samu magudi a gudanarwar zabe

- Omolubi ya bayyana cewa akwai bukatar ayi bayani domin kada rayuwar sauran masu zabe ya kasance cikin hatsari a tsarin

- Jigon na PDP yace furucin da Shugaban kasa Buhari yayi akan satar akwatin zabe na da matukar hatsari ga rayukan al’umma a lokacin gudanarwar zabe mai zuwa

Cif Newuwumi Omolubi, wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi karin haske akan lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi idan har aka samu magudi a gudanarwar zabe.

Ya mika wannan bukata ne domin samun karin hasken a wani taron manema labarai a rtanar Juma’a 22 ga watan Fabrairu cewa akwai bukatar ayi bayani domin kada rayuwar sauran masu zabe ya kasance cikin hatsari a tsarin, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sai kayi bayanin lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi – Jigon PDP ga Buhari

Sai kayi bayanin lokacin da ya kamata sojoji su yi harbi – Jigon PDP ga Buhari
Source: Facebook

Jigon na PDP wanda ya kasance mamba a kwamitin kamfen din jam’iyyar a Warri ta arewa da ke jihar Delta yace furucin da Shugaban kasa Buhari yayi akan satar akwatin zabe na da matukar hatsari ga rayukan al’umma a lokacin gudanarwar zabe mai zuwa.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kungiyar kamfen din gida-gida na jamiyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ilori ya bayyana cewa umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro na su yi hukuncin ba sani-ba sabo ga wadanda suka sace akwatin zabe a lokacin zaben kasar hanya c eta hana afkuwar hakan a lokacin zabe.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 8 da Buhari ya fadi a jawabin da yayiwa jama’a gabannin zaben Shugaban kasa

Yace furucin Shugaban kasar zai magance yawan kasha-kashe da tashin hankali a lokacin zabe sannan zai hana ayi magudi a zaben wanda a cewarsa ta zamo rowan dare a zaben Najeriya.

Ilori, wanda yayi Magana a Akure, babbar birnin jihar Ondo, yayinda yakje jagorantar rangajin APC a yankuna daban-daban na jihar domin ci gaba da kamfen din gida-gida yace APC ta shirya gudanar da zabe na gaskiya da amana a zaben gobe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel