Muhimman abubuwa 8 da Buhari ya fadi a jawabin da yayiwa jama’a gabannin zaben Shugaban kasa

Muhimman abubuwa 8 da Buhari ya fadi a jawabin da yayiwa jama’a gabannin zaben Shugaban kasa

A ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2018 zasu zabi cigaba da gwamnati mai ci ko kuma sabuwar gwamnati don gudanar da ayyukan kasa. Yayinda yake bayani akan muhimmancin zaben da za a gudanar a ranar Asabar, shugaban kasa Buhari a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu, a lokacin da yake bayani ga al’umman kasa yayinda suke jiran ranar zaben.

Legit.ng ta kawo muku abubuwa 8 da shugaban kasa Buhari yayi tsokaci akansu yayinda yake jawabi ga al’umman kasa kafin ranar gudanar da zaben shugaban kasa.

Muhimman abubuwa 8 da Buhari ya fadi a jawabin da yayiwa jama’a gabannin zaben Shugaban kasa

Muhimman abubuwa 8 da Buhari ya fadi a jawabin da yayiwa jama’a gabannin zaben Shugaban kasa
Source: Depositphotos

Ga batutuwan kamar haka:

1. Gobe, za a bude zabe. Gobe muna da yardar cewa Najeriya za ta gane matsayinta a damokardiyya sannan kuma babu ruwan sauran kasashen duniya a wannan tafarkin da muka zaba wa kanmu.

2. Mutane da yawa sun kasance cikin damuwa akan yanda lamarin zaben zai zo da fitintinu. Ku karyata hakan tare da nuna musu cewa kun kasance mutane ne masu amimci, masu bin dokar soyayya da zaman lafiya, damokardiyya da hadin kan kasarmu.

3. Nayi amanna da cewa INEC ta san hakki da nauyin da ya rataya a wuyanta.

KU KARANTA KUMA: Satar akwatin zabe: Jigon APC ya kare Buhari kan umurnin da ya bayar

4. Ya zama wajibi mu ajiye kokwanto sannan muyi imani da cewa INEC za ta yi yadda ya kamata. Ya zama dole mu amince da kuma karfafa wa INEC gwiwa domin su cika hakkin kasa day a rataya a wuyansu.

5. A matsayina na Shugaban kasa, ina umuratan dukkanin yan Najeriya da ke da katin zabe das u fita su kada kuri’u a gobe domin isar da yancinsu. Ina umartanku na ku fita ku yi zabe.

6. Ka da ku ji tsoron rade-radin cewa rikici zai kaure. Hukumomin tsaron mu na aiki sosai domin tabbatar da ingantaccen tsaro.

7. Za ku yi zabe a bayyane kuma cikin zaman lafiya, ku ajiye tsoro da barazana.

8. Ku mutunta yancinku a matysayin masu zabe ta hanyar zuwa zabe a gobe domin zaben gwamnatin da kuke muradi, gwamnatin da za ta kai Najeriya inda take mafarkin zuwa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel